[Google Drive] Yadda Zaka Ajiye Files Dinka A Google Drive
Assalamu Alaikum Jama'a Barkanku da haduwa damu a cikin wannan darasin ,
Na Koyon yadda zaka ajiye Documents dinka a google drive cikin kwanciyar hankali.
Batare da bata lokaci ba , bari mu shiga cikin darasinmu, gadan- gadan.
Google Drive wurin ajiye bayanai ne kamar dai Memory Card dinka, zaka iya ajiye video, audio da ma hoto da kuma sauran document dinka akai,
kamfanin google suka samar dashi a ranar 24 ga watan April na shekara ta 2012, ana iya mafani dashi a waya da kuma Computer.
Za ka iya saka wani file dinka akai sannan ka baiwa mutum link dinsa shima ya sauke ma’ana dai zaka iya turawa mutum wani file ta google drive.
Google Drive suna bada Gigabytes 15 kyauta ga duk wanda ke amfani da account na google ma’ana idan kana da Gmail to ka mallaki Gigabytes 15 a Google Drive dinka,
idan mutum yana son sama da haka to kamfanin google suna siyarwa ma’ana zaka biya kudi, Google Drive yana amfani ne da Data wajen sanyawa da kuma sauke abu akai.
Yadda Ake Amfani Da Google Drive:
Yadda ake amfani dashi a Computer:
Zaka ziyarci www.drive.google.com
Sai ka yo uploading din files dinka da kake son ajiyewa akan Drive din.
Sai kayi sharing in kana so ma’ana ka fitar da link dinsa yadda zaka iya baiwa wani ya sauke, ko kuma ka gyara wani abun aciki.
Yadda Ake Amfani dashi a waya:
Ka shiga application mai suna “Drive” wanda yake cikin jerin application da mafiya yawa android tana zuwa dasu sai dai da yawa mutane ba’a amfani dashi, ko kayi searching dinsa a Play Store.
Idan ka shiga anan zaka gani idan ka sanya gmail dinka akan wayar kai tsaye zai budo maka idan ma kana da files akai zaka gani.
Akwai alamar + wadda itace zaka danna domin dora sabbin files dinka.
Akwai menu dinsa kamar sauran app a gefe.
- Amfanin Google Drive:
Amfani da files dinka a duk sanda kake so a ko ina kake,
misali ina Kano sai na ajiye files dina a Drive wataran ina Abuja sai bukatar wannan files din ta taso to kawai zanyi login a drive ne koda ba a wayata bane na sauke wannan files din.
Aikawa da wasu sakonka ta nan ta yadda zaka iya baiwa mutum dama ya sauke wani sako da kake son tura masa misali daga nan Nigeria zaka iya turawa mutumin da yake London sakon wasu files daga nan.
Yin aiki da Document dink aba tare da network ba “Work Offline” akwai inda zaka shiga ka tsara files dinka a menu na Google Drive su zama zaka iya amfani dasu koda baka Network (Data) ma’ana bayan kayi Uploading.
Backup na files dinka misali idan zaka sake installing WhatsApp zaka ga ya baka dama ka dawo da tsohon chat dinka wanda shima yana adana maka shi ne a wancan Drive din naka.
Zaka iya yin searching na duk wani file da ka ajiye a Drive din.
Zaka iyi yin Scanning ko Snapping na Credential dinka ko wasu takardunka masu muhimmanci ka adanasu a Drive.
Yana adana maka duk wani sako da ya hada da hoto sauti ko document da aka aika maka dashi ta gmail dinka, ko bayan tsawon lokaci idan kaje Drive zaka ga wannan sakon.
Kuci gaba da kasance damu akoda yaushe.
Comments
Post a Comment