Posts

Showing posts from December 23, 2018

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES

Image
ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES   P-Yes ko Presidential Youth Empowerment Scheme shiri ne da ofishin Shugaban Kasa ya kirkiro karkashin Jagorancin Mai baiwa shugaban Kasa Shawara na Musamman akan Harkokokin Matasa da Dalibai.   ABIN BURGEWA GA SHIRIN Wani abin burgewa da Shirin shine yadda aka zabo kananan Sana'oi da al'umma ke bukata a ko wace rana, a ko wace unguwa, Ko wane Gari, Ko wane Kauye. Sana'oi ne da Matashi zai iya yi ko ina, a ko wane lokaci. Dare ko Rana, Sanyi ko Zafi, Rani ko Damina   Sana'oin Basu bukatar Kama shago. Kawai matashi na bukatar dan Inda zai raba ne, kamar gefen titi, ko runfar kasuwa, koma cikin gida don gudanar da sana'ar shi.   MENENE MANUFAR SHIRIN Manufar shirin P-Yes shine; 1) Samarwa Matasa ayyukan yi don dogaro da kawunansu 2) Rage Yawan aikata miyagun Laifuffuka da Shaye Shayen Kwayoyi tsakanin Matasa ta hanyar samar masu da ayyukan yi. 3) Rage fatara da talauci da zaman kashe wando tsakanin Matasa. 4) H...

Menene Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa

Image
Menene Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa Menene Katin Zabe? Katin Zabe (Voters Card) shine katin da zai baiwa duk wani dan Nigeria mai shekaru Sha Takwas (18) zuwa sama damar kada kuri’ar sa a matakan zaben Shugaban kasa, Gwamna, ‘Yan Majalisun jiha, tarayya da Dattijai, shugaban karamar hukuma da Kansiloli. Abubuwan Da Ake Yi Da Katin Zabe Baya ga yin zabe kuma ana amfani da katin zabe wajen register wani abu na hukumomi, ko bankuna da sauran duk wani abu da ake yi da Valid ID Card. Su Waye Ke Yin Katin Zabe? Hukumar zabe ta kasa itace ke da alhakin yiwa ‘yan kasa katin zabe. Ana Biyan Kudi Domin Yin Katin Zabe? A’a katin zabe kyauta ne ba’a bada ko sisi duk wanda ya karbi kudinka da sunan katin zabe to ka wurgashi ga mahukunta. Su Waye Ya Halatta Suyi Katin Zabe? Duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 18 zuwa sama to shine ke da ‘Yancin yin katin zabe. Yaushe Ake Yin Katin Zabe? Yanzu ba kamar shekarun baya ba da ba’a yin katin zabe sai lokacin da zabe ya karato a’a yanzu kowane lokaci m...

Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Image
Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000 Shin Kana da Damuwa Da Yadda Ake Gudanar Da Ayyukan Gwamnati A Inda Kake, Kuma Ba Ka da Damar Daukan Mataki Akai? Ko Kuma Aikin Rashawa Ka Gano Ka Ke Son A Magance Shi A Matsayin Ka Na Me Kishin Kasa . In kuwa haka ne toh, kwantar da hankalin ka don kuwa cibiyar nan ta bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato( CITAD) da taimakon gidauniyar MacArthur sun shirya tsaf don kawo karshen wannan damuwar taka ta hanyar isar da damuwar ka ga mahukunta. Sun samar da wani sabon tsari mai suna “Report a Project” shi ne sabon tsarin da wadannan cibiyoyi suka bullo da shi don kawo karshen wulakantar da ayyuka da gwamnatoti ce kiyi , ko kuma yin su bada inganci ba dama uwa uba batun bankado badakalar cin hanci da rashawa ta hanyar baiwa matasa dalibi damar shigar da rahoton duk wani batun dake da alaka da abin da muka ambata a baya. Abin sha’awa kuma shine zaka iya rubutawa da tura rahotanka cikin harshen Hausa ko Turanci English. TAGOMASHIN DA ZA...

Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019

Image
Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019 Shin kana shirin fara kasuwanci ta Social Media? Ko kuma kana son kayi amfani da Social Media domin tallata sana’arka? Ka shirya cin moriyar social media a shekarar 2019 mai zuwa? A yau ina tafe da muhimman abubuwa shida da yakamata ka sani kafin fara kasuwancin social media. 1. Tsari:- Dole kayi nazari domin tsara shin me zaka iya yi a social media wanda zai iya daukar hankalin jama’a? Misali Sharfadi.com ta maida hankali akan harkar internet da computer. 2. Shiri:- Bayan tsari to dole ka shirya abinda zakayi misali zanyi magana akan internet, to ina so inyi rubutun (post), wannan rubutun shine kaya na (content) Ko kuma idan wani abun nake siyarwa to wannan abun shine kayana. 3. Sanyawa:- Bayan ka tsara ka shirya abu na gaba shine sanya kayan naka Idan misali a facebook ne kayi posting dinsa, idan instagram ne shima haka d.s. 4. Targeting:- Shine ka tsara wadanda kake son sakonka ya isar garesu misali ina siyar da Takalmi na...

Yadda Zaka Boye Ranar Haihuwarka A Facebook

Image
RANAR HAIHUWARKA A FACEBOOK Dan uwa yana da kyau ka rufe ranar haihuwarka da ka sanya a #Facebook ta zamo babu mai iya ganinta sai kai kadai, sannan ka tabbatar ka rike nawa ga wata ne da shekarar da ka saka domin wasu ba hakikanin na gaskiya suke sakawa ba. Masu satar account suna amfani dashi. Yadda ake rufewa shine: Kayi amfani da browser ka hau facebook dinka sai ka shiga “profile” sannan ka shiga “about” sai kaje wajen “Date Of Birth” a gefe zaka ga “edit” sai ka shiga zaka wajen alamar nan ta “privacy” idan ka shiga zaka ga “public” “friend” “only me” sai ka zabi “only me”. Mungode.

[Facebook] YADDA ZAKA CANJA SUNAN KA NA FACEBOOK

Image
((YADDA ZAKA CANJA SUNAN KA NA FACEBOOK)) Jama’a Assalamu Alaikum da fatan kuna cikin koshin lafiya acikin shirin mu na wannan lokaci shiri na bakwai (8) zanyi bayani akan yadda ake canja suna a facebook, sai ku biyo mu, 1. YADDA ZAKA CANJA SUNA A FACE BOOK SHINE:- a. Ka shiga “settings & privacy” b. Daga nan sai ka shiga “general” c. Daga nan sai ka shiga “name” d. A gefe za kaga “edit” sai ka shiga e. Zai baka gurabe guda uku (3) i. First name (suna na farko) ii. Middle name (suna na tsakiya) iii. Last name (suna na uku) f. Sai ka cike sunan da kake so g. A kasa sai ka danna “review change” shi kenan zai kara baka zabi na sunan sai ka zabi wanda ka ke so, 2. ABUBUWAN DA YA KAMATA KA SANI GAME DA CANJA SUNA A FACEBOOK:- a. Ka sani cewa Idan ka canja suna to baka da damarkara canja sunan sai bayan kwanaki sittin (60) b. Idan kazo saka sunan akwai abubuwan da ba’a sakawa sune kamar haka: i. Alamomin rubutu, ii. Ko ka hargitsa haruffan karamin baki da babban baki iii. Ko mai-mai ta h...

YADDA AKE BUDE EMAIL

Image
((YADDA AKE BUDE EMAIL)) Jama’a Assalamu Alaikum da fatan kuna cikin koshin lafiya acikin shirin mu na wannan lokaci shiri na bakwai (7) zanyi bayani akan yadda ake bude email, sai ku biyo mu, Email: wanda ake kira a turance da Electronic Mail: tamkar wani adreshi ne naka na yanar gizo-gizo ko wani gida naka da idan ana neman ka nan za’aje, idan za’a baka sako nan za’a tura maka, sannan kai ma idan zaka turawa wani sako to sai ka shiga naka email din ka tura sakon, Sai dai email din nan akwai kala daban-daban ba wai guda daya bane, EMAIL DINA BIYU NE INA DA EMAIL KUMA INA DA GMAIL:-  wannan magana ce da dayawa mutane keyi wadda kuma kuskure ne, misali idan aka ce waya an san akwai waya iri-iri kamfani daban-daban amman duka sunan su waya, haka idan aka ce Mota kowa ya san mota kala-kala ce ba kala daya kawai ba, to idan akace email shima sunan su ne amman idan kace kana da email to kana bukatar yin bayanin shin wane iri ne email din? Gmail ne ko Hotmail, Yahoo da sauran su, ba wai ...

Shin Ko Kasan Ma’anar Google?

Image
Shin Ko Kasan Ma’anar Google?Menene Google? Google kamfanine na ‘yan kasar Amurka wanda ke hada-hadar kimiyar yanar gizo da Computer, Google yana baka dama ka binciki duk abinda kake so ka bincika a duk sanda kake so, shi kuma ya baka bayani akai, a hausance ana kiransa da Matambayi Baya Bata. Tarihin Google Account: Mr. Larry Page da Mr. Sergey Brin suka samar da Google a shekarar 1998 a lokacin da suke karatun PhD a jami’ar Stanford University dake Califonia Sakatariyar Google tana birnin California izuwa yanzu shekara ta 2018 Google yana da ma’aikata guda Dubu Tamanin da Biyar da Hamsin 85,050. Menene Google Account? Google Account shine ka mallaki account a kamfanin google wato dai kayi register dasu. Meye Alakar Google Account da Gmail Account? Da Gmail da Google Account duka abu daya ne idan ka mallaki Email din Gmail to shine dai Google account domin na duka kamfani daya ne. Google Sarkine: Tabbas Google Sarkine shafin Google dake kan gaba a duniya yana da bangarori da dama birj...

Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google

Image
Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google Assalamu alaikum, a yau zamuyi magana akan yadda ake dora lambobin waya wato Contacts akan Google, sai a biyo mu. Menene Google Contact? Google Contact shine tsarin adana lambobin wayarka da kuma emails na mutanenka akan Google, Wanda hakan zai baka damar samun contact dinka koda kuwa ka yarda wayarka. Idan yanzu wayarka babu caji kuma kana son ka dauki lambar wani daga cikin lambobinka to kawai zaka iya karbar wayar abokinka kayi login a Google dinka shike nan zaka ga lambobinka. Kuma yana cin lambobi ba adadi fiye da layin waya. Ta Yaya Zaka Mallaki Google Contact? Domin samun damar amfani da google contact abinda kake bukata shine account na Google.   Bayan ka mallaki wannan account din to shikenan kana da damar ajiye dukkan contacts dinka akan mail. Yadda Zaka Ajiye Contacts Dinka a Google Shine: 1. Da farko zaka dora google account dinka akan wayar. 2. Sai ka shiga contact dinka na waya sai ka danna alamar “options” 3. Zai baka “Imp...

Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp

Image
Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp Bayan gaisuwa da fatan kowa yana lafiya, yau a darasin mu  zamu yi magana akan Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp, sai a biyo mu. Idan kana so ka kumbura rubutu a WhatsApp to zaka yi amfani da alamar * ka sanya ta a farko da kuma karshen inda kake son kumburawar misali: Ina son rubuta Basheer sai na saka *Basheer+ * amman sai na cire wannan + din zai koma * a Kunbure, Idan ina son na karkatar da rubutun kuma sai nayi amfani da alamar Basheer+ sai na cire + din zai koma Basheer Idan ina so na ja layi akan rubutun kuma sai nayi amfani da alamar ~ misali ina son na saka tambarin Naira ~N+~ amma sai na cire + din zai koma ~N~ Idan ina so na canja tsarin rubutun daga wanda nake amfani dashi kuma sai nayi amfani da guda uku misali Basheer + sannan guda uku ake sakawa. Sai ka cire + zai baka ““Basheer“` . Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba. Domin samun sauran rubutukan da suka gabata sai ka ziyarci www.sharfadi.com Mungode

[Karanta Yanzu] Yadda Zaka Nemi Katin Dan Kasa Ta Wayarka

Image
[Karanta Yanzu] Yadda Zaka Nemi Katin Dan Kasa Ta Wayarka Menene Katin Dan Kasa? Shine kati/takardar shaidar cewa mutum dan Nigeria ne. Matsayin Katin Dan Kasa: Katin dan kasa wajibine akan duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 16 zuwa sama a duniya. Ana Zama Dan Nigeria Ta Hanyoyi Kamar Haka: 1. Wanda aka haifa a Nigeria ko da kuwa Iyayensa ba ‘yan Nigeria bane indai an haifeshi a Nigeria. 2. Wanda aka haifa daga ranar samun ‘yan cin kai. 3. Wanda aka haifa a wata kasar amman iyayensa ‘yan Nigeria ne, ko kuma daya daga cikin Iyayensa. 4. Dan kasar waje da ya auri ‘yar Nigeria, sai ya dawo Nigeria da zama, shima zai zama dan Nigeria. 5. Wanda shugaban kasa ya bashi shaidar cewa ya zama dan kasa (sai dai wannan ban sani ba ko za’a iya yi masa katin dan kasa). Yadda Ake Yin Register Katin Dan Kasa: Akwai hanyoyi guda biyu da ake register katin dan kasa sune kamar haka: *Hanya Ta Farko* Ka nema ta waya ko ta computer dinka. *Kaje shafinsu wato  https://www.nimc.gov.ng *Sai ka shiga “...