Posts

AMFANIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR JIKI

Image
 Namijin goro wani muhimmin abu ne daga cikin kayayyakin da ke da sanadarai masu taimaka wa ga kiwon lafiyar jiki.    Daga ciki akwai: (1) YANA KASHE DAFIN MACIJI DA KUNAMA:    Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda daya ya ci, insha'Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin. (2) YANA KASHE MACIJI:   Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba'a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu. (3) YANA KASHE GUBA:   Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, a ba shi namijin goro guda daya ya cinye, insha'Allah zai amayar da gubar da ya sha. (4) YANA FITAR DA DUK WANI CUTA:   Ana yayyanka namijin goro a jika a rika sha, insha'Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita. (5) YANA KARA KARFI GA NAMIJI:   Ana cin namijin goro saboda da karin karfi ga masu iyalai 'yan mintuna kafin a ...

ZA'A HADE DANDALIN FACEBOOK, WHATSAPP DA INSTAGRAM

Image
   Dandalin sadarwa ta Facebook ta shirya hade tsarinsa na sakonni (Facebook Messager) a wajen daya da manya manyan dandalin nan shahararru na Whatsapp da Instagram.   Wannan zai Nada dama ga masu amfani da wadannan tsari wajen tafiyar da wadannan dandali a waje daya (App), domin za su samu damar tura sakonni kai tsaye zuwa ga wadannan dandaloli.    Tsarin ba yana nufin wani daga cikinsu zai bar ta sa tsarin bane, a'a su na nan a bisa tsarin su na da, Kowa yana cin gashin kansa, amma tsarin zai bada damar mu'amalantar wadannan dandali a wuri guda ba tare da sai mai amfani da su ya fita ba.   Jaridar New York Times ta rawaito cewa shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg shine ya jagoranci wannan hadin gwiwar, ya kuma ce wannan wani gagarumin aiki ne da ya dauki dogon lokaci yana tsara shi, wanda idan an kammala shi duk mai amfani da wadannan shafuka na sadarwa, zai samu damar amfani da su kai tsaye.   Wanda ya ce hakan na da matukar wuya domin ...

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

Image
   Idan aka ce "APP" (APPLICATION) ko "APK" (Android Package Kit) shine abubuwan da wayar ANDROID take amfani da shi don saukake aiki da wayar wajen tafiya kai tsaye ga abinda kake so Ka sarrafa a wayarka, kuma ana sa shi a waya har ma ayi musanyansu daga waya zuwa waya. Duk wayar ANDROID tana bukatar APK ko APPs don tafiyar da wayar, domin su ne za su taimakawa mai wayar wajen jin dadin amfani da wayar.    Akwai APPs masu yawan gaske da mai ANDROID zai iya amfani da su kamar na GAME, MUSIC, SOCIAL MEDIA, BANKING, BROWSERS,  da dai sauransu masu yawa.    Amma kuma bayan wadannan APPs masu amfani Ga mai ANDROID akwai wadanda suke ba su da amfani sosai, sai dai ma cutar da wayar maimakon amfanarwa.    Wasu daga cikin wadannan APPs din suna cutar da waya kai tsaye, wasu kuma a hankali suke cutar da wayar ba tare da mai wayar ya sani ba, sai bayan ta samu matsala.    Ga wasu daga cikinsu guda biyar kamar yadda bincike ya nun...

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES

Image
ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES   P-Yes ko Presidential Youth Empowerment Scheme shiri ne da ofishin Shugaban Kasa ya kirkiro karkashin Jagorancin Mai baiwa shugaban Kasa Shawara na Musamman akan Harkokokin Matasa da Dalibai.   ABIN BURGEWA GA SHIRIN Wani abin burgewa da Shirin shine yadda aka zabo kananan Sana'oi da al'umma ke bukata a ko wace rana, a ko wace unguwa, Ko wane Gari, Ko wane Kauye. Sana'oi ne da Matashi zai iya yi ko ina, a ko wane lokaci. Dare ko Rana, Sanyi ko Zafi, Rani ko Damina   Sana'oin Basu bukatar Kama shago. Kawai matashi na bukatar dan Inda zai raba ne, kamar gefen titi, ko runfar kasuwa, koma cikin gida don gudanar da sana'ar shi.   MENENE MANUFAR SHIRIN Manufar shirin P-Yes shine; 1) Samarwa Matasa ayyukan yi don dogaro da kawunansu 2) Rage Yawan aikata miyagun Laifuffuka da Shaye Shayen Kwayoyi tsakanin Matasa ta hanyar samar masu da ayyukan yi. 3) Rage fatara da talauci da zaman kashe wando tsakanin Matasa. 4) H...

Menene Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa

Image
Menene Katin Zabe Da Yadda Ake Yinsa Menene Katin Zabe? Katin Zabe (Voters Card) shine katin da zai baiwa duk wani dan Nigeria mai shekaru Sha Takwas (18) zuwa sama damar kada kuri’ar sa a matakan zaben Shugaban kasa, Gwamna, ‘Yan Majalisun jiha, tarayya da Dattijai, shugaban karamar hukuma da Kansiloli. Abubuwan Da Ake Yi Da Katin Zabe Baya ga yin zabe kuma ana amfani da katin zabe wajen register wani abu na hukumomi, ko bankuna da sauran duk wani abu da ake yi da Valid ID Card. Su Waye Ke Yin Katin Zabe? Hukumar zabe ta kasa itace ke da alhakin yiwa ‘yan kasa katin zabe. Ana Biyan Kudi Domin Yin Katin Zabe? A’a katin zabe kyauta ne ba’a bada ko sisi duk wanda ya karbi kudinka da sunan katin zabe to ka wurgashi ga mahukunta. Su Waye Ya Halatta Suyi Katin Zabe? Duk wani dan Nigeria da ya kai shekara 18 zuwa sama to shine ke da ‘Yancin yin katin zabe. Yaushe Ake Yin Katin Zabe? Yanzu ba kamar shekarun baya ba da ba’a yin katin zabe sai lokacin da zabe ya karato a’a yanzu kowane lokaci m...

Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Image
Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000 Shin Kana da Damuwa Da Yadda Ake Gudanar Da Ayyukan Gwamnati A Inda Kake, Kuma Ba Ka da Damar Daukan Mataki Akai? Ko Kuma Aikin Rashawa Ka Gano Ka Ke Son A Magance Shi A Matsayin Ka Na Me Kishin Kasa . In kuwa haka ne toh, kwantar da hankalin ka don kuwa cibiyar nan ta bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato( CITAD) da taimakon gidauniyar MacArthur sun shirya tsaf don kawo karshen wannan damuwar taka ta hanyar isar da damuwar ka ga mahukunta. Sun samar da wani sabon tsari mai suna “Report a Project” shi ne sabon tsarin da wadannan cibiyoyi suka bullo da shi don kawo karshen wulakantar da ayyuka da gwamnatoti ce kiyi , ko kuma yin su bada inganci ba dama uwa uba batun bankado badakalar cin hanci da rashawa ta hanyar baiwa matasa dalibi damar shigar da rahoton duk wani batun dake da alaka da abin da muka ambata a baya. Abin sha’awa kuma shine zaka iya rubutawa da tura rahotanka cikin harshen Hausa ko Turanci English. TAGOMASHIN DA ZA...

Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019

Image
Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019 Shin kana shirin fara kasuwanci ta Social Media? Ko kuma kana son kayi amfani da Social Media domin tallata sana’arka? Ka shirya cin moriyar social media a shekarar 2019 mai zuwa? A yau ina tafe da muhimman abubuwa shida da yakamata ka sani kafin fara kasuwancin social media. 1. Tsari:- Dole kayi nazari domin tsara shin me zaka iya yi a social media wanda zai iya daukar hankalin jama’a? Misali Sharfadi.com ta maida hankali akan harkar internet da computer. 2. Shiri:- Bayan tsari to dole ka shirya abinda zakayi misali zanyi magana akan internet, to ina so inyi rubutun (post), wannan rubutun shine kaya na (content) Ko kuma idan wani abun nake siyarwa to wannan abun shine kayana. 3. Sanyawa:- Bayan ka tsara ka shirya abu na gaba shine sanya kayan naka Idan misali a facebook ne kayi posting dinsa, idan instagram ne shima haka d.s. 4. Targeting:- Shine ka tsara wadanda kake son sakonka ya isar garesu misali ina siyar da Takalmi na...