ZA'A HADE DANDALIN FACEBOOK, WHATSAPP DA INSTAGRAM
Dandalin sadarwa ta Facebook ta shirya hade tsarinsa na sakonni (Facebook Messager) a wajen daya da manya manyan dandalin nan shahararru na Whatsapp da Instagram. Wannan zai Nada dama ga masu amfani da wadannan tsari wajen tafiyar da wadannan dandali a waje daya (App), domin za su samu damar tura sakonni kai tsaye zuwa ga wadannan dandaloli. Tsarin ba yana nufin wani daga cikinsu zai bar ta sa tsarin bane, a'a su na nan a bisa tsarin su na da, Kowa yana cin gashin kansa, amma tsarin zai bada damar mu'amalantar wadannan dandali a wuri guda ba tare da sai mai amfani da su ya fita ba. Jaridar New York Times ta rawaito cewa shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg shine ya jagoranci wannan hadin gwiwar, ya kuma ce wannan wani gagarumin aiki ne da ya dauki dogon lokaci yana tsara shi, wanda idan an kammala shi duk mai amfani da wadannan shafuka na sadarwa, zai samu damar amfani da su kai tsaye. Wanda ya ce hakan na da matukar wuya domin ...