YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA
Kamar yadda ka sani masu amfani da wayar android suna fama da irin wannan matsala na bude data da kanta batare da ka budeba, irin wannan matsalar tana 6atawa mutane rai haka kawai ka rufe datar wayarka bayan wani dan lokaci kawai saika tarar ta bude kanta idan ta bude kuma idan wayar da mb ko kudi nan take zakaga wasu apps din sun bude kansu suna amfani da mb ganin data ta budu sukuma apps sai suyi ta aiki. sannan idan data tana bude wayar zakaji tana daukan zafi kokuma ta dingama wani shirme na banza, to irin wannan matsalar Malware ne yake kawo irin wannan matsalar ita kuma malware, yawan janye janye wato download na kowane irin apps ko game suke suke kawato malware da kuma yawan Ture ture ta Xender sabo da wasu apps din suna zuwa da matsala to yawancinmu bama sanin hakan sai kawai da zarar munga apps masu kyau batare da wani dubawaba kawai saimu bukaci wannan apps din har a turo mana ko muyi download nasa, sannan idan muka samu apps din bama lura da...