Posts

Showing posts from November 11, 2018

Android] Yadda zakayi Amfani da wayar Android wajen Fitar da Amsar Lissafi(Mathmatic) ta hanyar Daukan Hoton Tambayar

Image
Ina kuke masu amfani da wayar Android shin kunsan zaku iya fitar da amsar lissafi/math ta hanyar daukan hoton tambayar da wayar android  sannan wayar ta fidda muku amsar dede, Abin babu wuya kawai idan kana da wayar android zaka iyayin hakan,  sannan android din ya kasance yana da Camera mai kyau, domin kuwa kawai Lissafin zaka Rubuta ajikin Littafi ko wata takarda saika haska da wayarka, nan take zakaga ta baka amsa dede, inde har kayi Rubutun dede to insha Allah zaka samu amsa,  yanzu abin da zakuyi kawai ku shiga Link dinnan ku dauko wannan Application mai suna PHOTOMATHS.   Download Photo Maths Apk    Bayan kunyi download na wannan application, sai kuyi install dinsa . sannan ku budeshi da zarar kun bude saiku duba daga samansa akwai wasu alamomi,  to saiku shiga Alamar Camera, da zarar kun shiga zai baku damar daukan tambayar, da kukeso ku, to saiku dauko Littafi ko wani takarda, saiku Rubuta tambayar/lissafin ajiki, sannan saiku haska da wannan ...

YADDA ZAKADAWO DA FACEBOOK DIN DA AKA SACE

Image
YADDA ZAKADAWO DA FACEBOOK DIN DA AKA SACE Assalamu Alaikum, Barkanku Dai Jama'a, yau zanyi Bayani akan yadda ake dawo da account din facebook da akayi hacking, Ma'ana Aka Sace Shi. Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen dawo da account na facebook amman zamu dauki wannan kasancewarta mafi sauki. 1. Idan ka tabbatar anyi hacking din account dinka to sai ka shiga wannan link din: Facebook.com/hacked Sai ka saka email dinka ko lambar wayarka ko kuma cikakken sunanka na facebook 2. Bayan ka saka zai nuno maka ka sanya password dinka, sai ka sanya password din da ka sani kafin a kwace maka account din. 3. Bayan ka saka zai nuna maka alamar chanja password “reset my password” sai ka shiga. 4. Daga nan zasu nuna maka email wanda ka san tuni hackers sun canja shi ko kuma email dinka ne ma amman yanzu ka manta password din to anan sai ka danna “no longerlonger access to these?” 5. Daga nan zasu nuna maka “Now write your new email address that you want to send the change password linklin...

Yadda Zaka Nemi Aikinyi A Garinku Ta Google

Image
Yadda Zaka Nemi Aikinyi A Garinku Ta Google Jama’a assalamu alaikum yau a darasinmu na 47 za muyi magana akan yadda mutum zai yi amfani da google wajen neman aikin yi a garinsu, sai a biyo mu. Kamar yadda muka sani, Google yana da bangarori da dama wadanda kuma suna da matukar muhimmanci mutum ya sansu domin cin gajiyarsu to daga ciki shine wannan tsarin da zai baka dama ka san wasu wurare dake neman ma’aikata a kusa da kai. Yadda Zaka Nemi Aiki Ta Hanyar Google Shine : 1. Da farko kana bukatar ka mallaki account na Google domin basu damar baka Ingantaccen bayani: 2. Abu na biyu shine ka dora google account din akan wayarka ko computer dinka. 3. Abu na uku shine sai ka shiga Google wato www.google.com 4. Sai ka rubuta “Jobs near me” 5. Shikenan zai budo maka sabon shafi. A saka zaka ga ya rubuta maka yankin da kake. Sai kuma jerin damarmakin aiki a kasa, sai mutum ya duba ya ga me ake bukata da kuma abu na gaba da ake bukatar yayi. Allah ya bada sa’a.