Yadda Zaka Nemi Aikinyi A Garinku Ta Google

Yadda Zaka Nemi Aikinyi A Garinku Ta Google

Jama’a assalamu alaikum yau a darasinmu na 47 za muyi magana akan yadda mutum zai yi amfani da google wajen neman aikin yi a garinsu, sai a biyo mu.

Kamar yadda muka sani, Google yana da bangarori da dama wadanda kuma suna da matukar muhimmanci mutum ya sansu domin cin gajiyarsu to daga ciki shine wannan tsarin da zai baka dama ka san wasu wurare dake neman ma’aikata a kusa da kai.

Yadda Zaka Nemi Aiki Ta Hanyar Google Shine :

1. Da farko kana bukatar ka mallaki account na Google domin basu damar baka Ingantaccen bayani:


2. Abu na biyu shine ka dora google account din akan wayarka ko computer dinka.

3. Abu na uku shine sai ka shiga Google wato www.google.com

4. Sai ka rubuta “Jobs near me”

5. Shikenan zai budo maka sabon shafi.

A saka zaka ga ya rubuta maka yankin da kake.

Sai kuma jerin damarmakin aiki a kasa, sai mutum ya duba ya ga me ake bukata da kuma abu na gaba da ake bukatar yayi.

Allah ya bada sa’a.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES