Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019

Abubuwa 6 Ga Wanda Zai Fara Kasuwanci Ta Social Media A 2019

Shin kana shirin fara kasuwanci ta Social Media? Ko kuma kana son kayi amfani da Social Media domin tallata sana’arka?

Ka shirya cin moriyar social media a shekarar 2019 mai zuwa?

A yau ina tafe da muhimman abubuwa shida da yakamata ka sani kafin fara kasuwancin social media.

1. Tsari:- Dole kayi nazari domin tsara shin me zaka iya yi a social media wanda zai iya daukar hankalin jama’a? Misali Sharfadi.com ta maida hankali akan harkar internet da computer.

2. Shiri:- Bayan tsari to dole ka shirya abinda zakayi misali zanyi magana akan internet, to ina so inyi rubutun (post), wannan rubutun shine kaya na (content) Ko kuma idan wani abun nake siyarwa to wannan abun shine kayana.

3. Sanyawa:- Bayan ka tsara ka shirya abu na gaba shine sanya kayan naka Idan misali a facebook ne kayi posting dinsa, idan instagram ne shima haka d.s.

4. Targeting:- Shine ka tsara wadanda kake son sakonka ya isar garesu misali ina siyar da Takalmi na ‘yan shekaru 22 to zan nemi iya masu wannan shekarun su gani, ko kuma kayan yara sai in nemi ‘yan shekaru irin na iyaye.

Haka bayan shekaru ana iya tagging din Jinsi idan kayan maza ne ka tallatawa maza ko kuma na mata d.s.

5. Bunkasawa:- Shine (promotion) a turance wato yadda zaka tallata kayanka ya samu jama’a sosai, irin wannan tsarin shine zaka biya kudi a tallata maka hajarka idan kayi post a wall dinka ana samun mutane 5 to idan kayi promotion zaka samu mutane 50 misali.

6. Auna Riba: Bayan kabi wadancan matakan to abu na karshe kana bukatar ka dinga lissafawa shin wane irin tasiri ka samu a yanzu da kuma da a kasuwancinka.

*Duka wadannan abubuwa shida suna bukatar fadada bayani akansu, kuma InshaAllah wataran zamu fadada.

Basheer Sharfadi

Social Media Strategist.

December, 2018.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES