Shin Ko Kasan Ma’anar Google?

Shin Ko Kasan Ma’anar Google?Menene Google?

Google kamfanine na ‘yan kasar Amurka wanda ke hada-hadar kimiyar yanar gizo da Computer, Google yana baka dama ka binciki duk abinda kake so ka bincika a duk sanda kake so, shi kuma ya baka bayani akai, a hausance ana kiransa da Matambayi Baya Bata.

Tarihin Google Account:

Mr. Larry Page da Mr. Sergey Brin suka samar da Google a shekarar 1998 a lokacin da suke karatun PhD a jami’ar Stanford University dake Califonia

Sakatariyar Google tana birnin California izuwa yanzu shekara ta 2018 Google yana da ma’aikata guda Dubu Tamanin da Biyar da Hamsin 85,050.

Menene Google Account?

Google Account shine ka mallaki account a kamfanin google wato dai kayi register dasu.

Meye Alakar Google Account da Gmail Account?

Da Gmail da Google Account duka abu daya ne idan ka mallaki Email din Gmail to shine dai Google account domin na duka kamfani daya ne.

Google Sarkine:

Tabbas Google Sarkine shafin Google dake kan gaba a duniya yana da bangarori da dama birjik, wanda idan ka mallaki account dinsu to ka mallaki duka wadannan sai dai mutanenmu da yawa basu san wadannan bangarorin ba, zamu dauki wasu daga ciki masu muhimmanci ga al’umma muyi bayaninsu.

By: Sharfadi.Com

Mungode

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES