[Wata Sabuwa] Ana Zargin Google Da Yin Batanci Ga Shugaban Amurka Donal Trump

[Wata Sabuwa] Ana Zargin Google Da Yin Batanci Ga Shugaban Amurka Donal Trump


Wani dan majalisar dokokin Amurka ya gabatar da korafi a gaban majalisar dokokin kasar dangane da yadda idan mutum yayi amfani da shafin Google (Matambayi baya bata) ya tambayi kalmar "Idiot" wawa ko sakarai a harshen Hausa sai Google din ya bashi amsa da hotunan shugaban kasar Amurka wato Donal Trump. 


Wannan korafin ya sanya majalisar gayyatar shugaban kamfanin na GOOGLE Mr. Sundar Pichai kan ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi akan wannan batu. 


Hakan kuwa akayi sai dai Mr. Pichai ya bayyana cewa sufa ko kadan ba sune suka kar zomon ba, hassalima rataya kawai aka basu. 


Domin kuwa ya bayyana cewa duk sanda mutum ya tambayi wani abu a shafinsu to ba sune suke dauko amsa su bashi ba, a'a kawai su shafinsu yana tattara bayanai ne da aka wallafa a shafukan internet masu alaka da abinda mutum ya tambaya.


Don haka su sam basu da hannu wajen bayyana hoton Mr. Trump a matsayin Sakarai. 


Hausawa sukace gani ya kori ji kaima zaka iya gwadawa a wayarka ka binciki kalmar "idiot" a Google kaga amsar da zai baka. 


Allah ya kyauta. 


Basheer Sharfadi 

Social Media Strategist. 

17-12-2018.


Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES