Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp
Bayan gaisuwa da fatan kowa yana lafiya, yau a darasin mu zamu yi magana akan Yadda Ake Canja Salon Rubutu A WhatsApp, sai a biyo mu.
Idan kana so ka kumbura rubutu a WhatsApp to zaka yi amfani da alamar * ka sanya ta a farko da kuma karshen inda kake son kumburawar misali:
Ina son rubuta Basheer sai na saka
*Basheer+ *
amman sai na cire wannan + din zai koma * a Kunbure,
Idan ina son na karkatar da rubutun kuma sai nayi amfani da alamar Basheer+ sai na cire + din zai koma Basheer
Idan ina so na ja layi akan rubutun kuma sai nayi amfani da alamar ~ misali ina son na saka tambarin Naira ~N+~ amma sai na cire + din zai koma ~N~
Idan ina so na canja tsarin rubutun daga wanda nake amfani dashi kuma sai nayi amfani da guda uku misali Basheer + sannan guda uku ake sakawa. Sai ka cire + zai baka ““Basheer“` .
Zamu dakata anan sai a rubutu na gaba.
Domin samun sauran rubutukan da suka gabata sai ka ziyarci www.sharfadi.com
Mungode
Comments
Post a Comment