Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google
Yadda Zaka Dora Lambobin Wayarka Akan Google
Assalamu alaikum, a yau zamuyi magana akan yadda ake dora lambobin waya wato Contacts akan Google, sai a biyo mu.
Menene Google Contact?
Google Contact shine tsarin adana lambobin wayarka da kuma emails na mutanenka akan Google, Wanda hakan zai baka damar samun contact dinka koda kuwa ka yarda wayarka.
Idan yanzu wayarka babu caji kuma kana son ka dauki lambar wani daga cikin lambobinka to kawai zaka iya karbar wayar abokinka kayi login a Google dinka shike nan zaka ga lambobinka.
Kuma yana cin lambobi ba adadi fiye da layin waya.
Ta Yaya Zaka Mallaki Google Contact?
Domin samun damar amfani da google contact abinda kake bukata shine account na Google.
Bayan ka mallaki wannan account din to shikenan kana da damar ajiye dukkan contacts dinka akan mail.
Yadda Zaka Ajiye Contacts Dinka a Google Shine:
1. Da farko zaka dora google account dinka akan wayar.
2. Sai ka shiga contact dinka na waya sai ka danna alamar “options”
3. Zai baka “Import/Export” sai ka shiga.
4. Zaka ga “Copy contacts from” ma’ana ka zabi daga inda zaka kwashi contact din naka, misali idan suna kan sim 1 sai ka zabi sim 1.
5. Sai ka danna “Next”.
6. Zai kawo maka “copy contacts to” ma’ana inda kake son ka mayar da contacts dinka, zaka ga suna google account dinka a sama sai ka zabe shi.
7. Daga nan sai ka danna “Next”.
8. Zai nuna maka “0 selected” ma’ana baka zabi ko guda daya ba, sai ka shiga ka zabi “select all” Shikenan zai zabi gabaki dayan contact dinka.
9. Sai ka danna “ok”
0. Shikenan contact dinka zaiyi copy zuwa kan email dinka.
A nan Zamu dakata sai a rubutu na gaba.
By: Sharfadi.Com
Mungode.
Comments
Post a Comment