Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Yadda Zaka Kayi Rubutu Da Hausa A Baka N30,000

Shin Kana da Damuwa Da Yadda Ake Gudanar Da Ayyukan Gwamnati A Inda Kake, Kuma Ba Ka da Damar Daukan Mataki Akai?

Ko Kuma Aikin Rashawa Ka Gano Ka Ke Son A Magance Shi A Matsayin Ka Na Me Kishin Kasa .

In kuwa haka ne toh, kwantar da hankalin ka don kuwa cibiyar nan ta bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato( CITAD) da taimakon gidauniyar

MacArthur sun shirya tsaf don kawo karshen wannan damuwar taka ta hanyar isar da damuwar ka ga mahukunta.

Sun samar da wani sabon tsari mai suna

“Report a Project” shi ne sabon tsarin da wadannan cibiyoyi suka bullo da shi don kawo karshen wulakantar da ayyuka da gwamnatoti ce kiyi , ko kuma yin su bada inganci ba dama uwa uba batun bankado badakalar cin hanci da rashawa ta hanyar baiwa matasa dalibi damar shigar da rahoton duk wani batun dake da alaka da abin da muka ambata a baya.

Abin sha’awa kuma shine zaka iya rubutawa da tura rahotanka cikin harshen

Hausa ko Turanci English.

TAGOMASHIN DA ZAKA IYA SAMU SAKAMAKON YIN WANNAN AIKIN:

In rahotan ka yai nasarar zamo wa mafi kyau akwai kyauta gwaggwaba. N30,000 wani kuma zai samu N20,000

Bugu da kari za’a sanya rahotan naka a cikin shirin da za’a gabatar a gidan rediyo.

Domin tura naka rahoton zaka sai ka danna kasa 👇 

http://www.reportaproject.ng

Allah ya bada sa’a ya taimaki kasar mu Najeriaya.

By: Sharfadi.Com


Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES