Za’a Fara Ganin Video Ba Tare Da Ka Danna Ba A YouTube
Shagala: {Za’a Fara Ganin Video Ba Tare Da Ka Danna Ba A YouTube}
A yayin da ake wani yanayin na gudun kece raini tsakanin manyan shafukan sada zumunta na Internet shima shafin YouTube dake zaman shafi na biyu a duniya wajen yawan masu amfani dashi tuni yayi nisa wajen zuwa nasa sabbin sauye-sauyen domin dai gamsar da masu amfani dashi.
Daga cikin sauye-sauyen da zai iya fara aiki kowane lokaci daga yanzu shine tsarin “Auto Play” tsarine wanda kana shiga YouTube sai kaga wani Video to ba sai ka shiga kan videon ba zaka ga yaya videon yake, a’a kawai tsayawa za kayi akan videon shi kuma zai fara haska maka “preview” kai tsaye ba tare da ka danna ba.
Zaka dinga ganin yadda videon yake idan yayi maka sai ka shiga idan kuma baiyi maka ba sai ka wuce, kamar dai yadda kuke gani a Instagram da kuma wadanda ke amfani da tsarin na “Auto Play” a dandalin facebook da kuma Instagram.
A makon da ya gabata ne kamfanin YouTube ya kaddamar da tsarin story mai tsawon mako guda a dandalin.
Allh ya taimaka.
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
Comments
Post a Comment