AMFANIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR JIKI


 Namijin goro wani muhimmin abu ne daga cikin kayayyakin da ke da sanadarai masu taimaka wa ga kiwon lafiyar jiki.
   Daga ciki akwai:
(1) YANA KASHE DAFIN MACIJI DA KUNAMA:
   Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda daya ya ci, insha'Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin.
(2) YANA KASHE MACIJI:
  Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba'a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu.
(3) YANA KASHE GUBA:
  Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, a ba shi namijin goro guda daya ya cinye, insha'Allah zai amayar da gubar da ya sha.
(4) YANA FITAR DA DUK WANI CUTA:
  Ana yayyanka namijin goro a jika a rika sha, insha'Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita.
(5) YANA KARA KARFI GA NAMIJI:
  Ana cin namijin goro saboda da karin karfi ga masu iyalai 'yan mintuna kafin a je ga iyalan.
(6) YANA MAGANIN CIWON GABABUWA:
  Cin namijin goro na magance matsalar ciwon gabobi, kamar yawan gullewa da zugi, yana kuma rage kowane irin radadin azaba.
(7) YANA MAGANIN (STD):
  Yawan cin namijin goro na kashe kwayoyin cutar da ake dauka wajen saduwa wato STD.
(8) YANA MAGANIN HUHU: Cin namijin goro na kara lafiyar huhun dan-Adam....
(9) YANA GINA GARKUWAR JIKI:
  Namijin goro na da kaso mai yawa na sinadarin 'antioxidant' wanda ke da muhimmancin gaske wajen yakar kwayoyin cututtuka da kuma sake gina garkuwar jikin dan-Adam.
(10) YANA MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO:
  Namijin goro rigakafi ne daga kamuwa da zazzabin cizon sauro....
(11) YANA KARE IDANU DAGA MAKANTA:
  Cin namijin goro na kare idanuwa daga makancewa....
(12) YANA KASHE GYAMBON-CIKI:
 Mai wannan larura idan yana cin namijin goro to insha' Allah zai warke....
 Allah Ya kara mana lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA ZAKA HANA WAYARKA TA ANDROID BUDE DATA DA KANTA

MANYAN APPS BIYAR (5) DA KE BATA MAKA WAYA

[Yi Regista Yanzu] ABINDA KUKE NEMAN SANI GAME DA SHIRIN P-YES