ZA'A HADE DANDALIN FACEBOOK, WHATSAPP DA INSTAGRAM
Dandalin sadarwa ta Facebook ta shirya hade tsarinsa na sakonni (Facebook Messager) a wajen daya da manya manyan dandalin nan shahararru na Whatsapp da Instagram.
Wannan zai Nada dama ga masu amfani da wadannan tsari wajen tafiyar da wadannan dandali a waje daya (App), domin za su samu damar tura sakonni kai tsaye zuwa ga wadannan dandaloli.
Tsarin ba yana nufin wani daga cikinsu zai bar ta sa tsarin bane, a'a su na nan a bisa tsarin su na da, Kowa yana cin gashin kansa, amma tsarin zai bada damar mu'amalantar wadannan dandali a wuri guda ba tare da sai mai amfani da su ya fita ba.
Jaridar New York Times ta rawaito cewa shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg shine ya jagoranci wannan hadin gwiwar, ya kuma ce wannan wani gagarumin aiki ne da ya dauki dogon lokaci yana tsara shi, wanda idan an kammala shi duk mai amfani da wadannan shafuka na sadarwa, zai samu damar amfani da su kai tsaye.
Wanda ya ce hakan na da matukar wuya domin tsarin kowane dandali dabam yake da na dayan, Saboda haka za'a dauki lokaci mai tsawo wajen aiwatar da tsarin, domin zai kai karshen wannan shekara ta 2019 ko ma ya kai cikin shekarar 2020 kafin a kammala.
A yanzu wadannan dandali za su ci gaba kamar yadda aka saba, amma cikekken tsarin kwakwaf na tafiyar da tsarinsu zai koma daya nan gaba. Ya ci gaba da cewa "Mutum hudu ne suke kokarin aiwatar da wannan hadin gwiwar, wanda zai hade wadannan manyan dandali uku na duniya a APP daya, wanda an kiyasta kimanin mutane biliyan biyu da miliyan dari shida (2.6 billion) suke amfani da su, idan aka hade su, mutane da dama za su samu damar sada zumunci a tsakaninsu kai tsaye".
Idan ba'a manta ba kwanakin baya, kamfanin sadarwa ta Whatsapp ta bada sanarwar tsari da take shirin kawowa na sanya tsaro na yatsa (fingerprint) a tsarin Whatsapp, don bada damar kariya ga masu amfani da dandalin, Saboda masu shiga ba tare da izini na.
Shi wannan tsari na tsaron yatsa (fingerprint) shine babban tsari da aka kawo wa APPs din waya mai manhajar ANDROID. Kuma zai bada damar samun cikekken tsaro ga mai ita daga masu shiga ba tare da izini ba.
Kuma wannan tsari yana nan tafe bada dadewa ba, Kamar yadda aka samu hakan a wasu APPs na bankuna kamar DIAMOND BANK.
A takaice duk lokacin da Ka zo shiga, zai nemi samfurin yatsarka kafin Ka shiga.

Masu hasashe sun ce kamfanin na Whatsapp har yanzu yana kokarin tsara wannan tsari na tantancewa tun da dadewa kuma kamar yadda aka sani, da ma babu shi a baya, Saboda haka ana kan kirkirarsa ne. A yanzu babu wata kafa da mutum zai tsare shafinsa
a Whatsapp.
Idan aka kirkiro wannan tsarin tsaron, za'a samu wani waje a gurbin tsarin tafiyar da Whatsapp (settings) inda masu amfani da shi za su kunnan wannan tsari ko kuma su kashe tsarin, wato a wajen *Settings>Account>Privacy* wanda a nan ne za'a kunna kamar yadda na gabatar.
Ana sa ran nan da wasu watanni za'a kammala wannan tsarin domin yana dab da kammaluwa. Kuma za'a samu wannan tsari a manhajin ANDROID da kuma iOS duka.
Har yanzu kamfanin Whatsapp tana kokarin kirkiro ingantacciyar hanya wajen zakulo sauti (audio), wanda zai bada damar karantawa da lissafa duk wani sauti da ke kan wayar mutum(memory) kafin ya tura wanda yake so zuwa ga wani ko wasu. Kuma zai samu damar sauraron sautin kafin ya tura kuma zai iya tura da yawa a lokaci guda.
Na Ku ILYASU SHUAIBU AHMAD
DANBAIWA MEDIA CONCEPT

Comments
Post a Comment